By Abbas Yakubu yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun, a ranar Alhamis, ta tabbatar da yin garkuwa da wasu ma’aurata a wani kauye dake karamar hukumar Obokun ta Osun, da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Osun, SP Yemisi Opalola, yace ma’auratan, London da Blessing Omoru, wasu ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa dasu a gonar su a daren ranar Laraba.
Opalola ya bayyana cewa an kai rahoton yin garkuwa da mutanen ne a ofishin ‘yan sanda na Esa-Oke kuma an tura tawagar ‘yan sanda da dabarun ceto wadanda aka sace.yace ‘yan sandan na hada kai da mafarauta da ’yan banga don tseratar da dazuzzukan daga hannun masu garkuwar, inda yace ‘yan sandan na kan bin sawun masu garkuwa da mutane.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya samu labarin cewa dan ma’auratan da aka yi garkuwa dasu, Andrew Omoru ya kai rahoton sace iyayensa ga ‘yan sanda.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa rundunar ‘yan sandan tace an kwato babur din ma’auratan da aka yi garkuwa dasu da harsashi sannan kuma babu kowa a wurin da lamarin ya faru, kuma suna nan suna kutsawa cikin masu garkuwa da mutanen.