Kwamishinan ‘yan sandan jihar Cross River, CP Aminu Alhassan a ranar Alhamis din nan ya tabbatar da sace wata dalibar lauya mai shekaru 24, Miss Dora Effiom daga gidanta da ke lamba 17 a kan titin Joseph Mkpang , a karamar hukumar Calabar ta jihar.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa masu garkuwa da mutanen sun tafi da yarinyar ne a cikin motar mahaifiyarta mai suna Grey Toyota Corolla, 2010 da misalin karfe 2:00 na ranar Larabar nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aminu Alhassan ya bayyana cewa rundunarsa ta Anti Cultism and Kidnapping Squad, karkashin jagorancin SP Awodi ta dauki matakin bankadowa tare da cafke wadanda ke da hannu wajen aikata wannan aika-aika.
Karanta kuma: Yan bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mambobin APC 3, Sun Kashe Wasu
Ya bayyana cewa, rundunar ba za ta bar wani abu ba wajen tabbatar da an gurfanar da duk wadanda ke da hannu a cikin gaggawa.
CP Aminu ya ce: “Ina so in yi amfani da wannan kafar domin sake gargadi wadanda ke Kuros Riba don aikata laifuka da su gaggauta ficewa daga jihar, domin babu wani mai laifi da zai tsira.
“Babu sauran mafaka ga duk wani mai laifi a Cross River, yanzu mun dauki matakin yaki zuwa duk wani yanki da aka sani da wanda ba a san shi ba.
“Ina so in tabbatar wa ‘yan jihar masu bin doka da oda da su gudanar da harkokinsu na halal ba tare da tsoro ba, mun riga mun gyara dukkan ayyukanmu, za a ceto yarinyar nan ba da dadewa ba, saboda muna kan hanyarmu yayin da muke magana,” CP Aminu ya tabbatar.
Binciken Vanguard ya nuna cewa maharan sun shiga gidan wacce abun ya shafa, mahaifin yarinyar da aka sace, Ntufam Francis Effiom da misalin karfe 1:00 na safe.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa Vanguard cewa ‘yan bindigar sun ji wa Ntufam Effiom rauni sosai, inda suka bar shi ya mutu bayan sun yi awon gaba da ‘yarsa, Deborah a cikin motar matarsa.
“An yi wa Ntufam Francis Effiom dukan tsiya, aka ji masa rauni kuma aka bar shi ya mutu, sannan suka dauko ‘yarsa a cikin wata mota kirar Toyota Corolla, mai launin toka, samfurin 2010 zuwa wani wuri da ba a sani ba.
“Amma zan iya gaya muku cewa nan ba da jimawa ba za a kama su, saboda muna kusa da su, in ji majiyar.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a kama wani ba, amma ana kokarin gano tushen lamarin.
A wani labarin kuma: Tinubu, Shettima Suna Nesanta Kansu Daga Gazawar Buhari – PDP
A ranar Alhamis ne jam’iyyar PDP ta ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da abokin takararsa, Kashim Shettima, suna hada baki da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin yaudarar ‘yan Najeriya gabanin zaben 2023.
Babbar jam’iyyar adawar ta ci gaba da cewa, Tinubu, Shettima da sauran jiga-jigan jam’iyyar APC na daukar matakan nesanta kansu daga gazawar da ake zargin gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta yi.