Daya daga cikin manyan masu jiran sarauta a Jordan Hamzah bin Hussein, na cikin mutanen da jami’an tsaro suka kama a wani samame kan wandanda ake zargi da yi wa tsaro barazana.
An ga tururuwan jami’an tsaro a yankin Dabouq da ke kusa da masarautar Jordan a wani bidiyo da aka wallafa a yanar gizo, inda tsohon Yeriman ya ce ‘yan sanda sun masa daurin talala a gida bayan da suka yi wa harabar gidansa kawanya.
Wani bidiyon da BBC ta samo daga lauyan Yeriman na ceewa, an kame wasu abokansa tare da janye masa jami’an tsaro da katse internet da wayoyin sadarwa a gidansa. Yeriman Hamzah bin Hussein ya musanta alaka da wata kungiya ko cin mutuncin masarautar, amma ya ce matakin baya rasa nasaba da sukar masarautar kan cin hanci da rashin daidai.