Rundunar Yan sandar Jihar Legas ta ce ta fara sauraren shari’ar wasu Jami’an ta biyar a rukunin gidaje na FESTAC da ake zargi da wawushe kudi har naira dubu dari biyu a hannun wani ɗan Najeriya mazaunin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato Dubai bayan da ya kawo ziyarar duba iyalan shi.
Ana zargin yan sandan ne da biyo mutumin ne yayin da yake tuka wata motar shi ta alfarma izuwa wurin wani cibiyar mu’amalar kuɗi ta banki wato POS inda suka bude Mishi ido dole sai da ya basu wanchan kudin.
Yanda labarin ya buwayi duniya dai shine sa’ilin da wata matashiya ta wallafa a shafin ta na Tuwita cewa wasu yan sanda sun biyo shi a garin FESTAC yayin da yake hanyar shi ta zuwa gida daga filin jirgin sama inda suka tsayar da shi tare da karɓar wannan makudan kudade.
Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar Muyiwa Adejobi wanda ya tabbatar da aukuwar wannan lamari ya shaida cewa dukkanin wadanda ake zargin suna chan an killace su a Shelkwatar rundunar dake birnin Ikko.
Adejobi ya ce bincike ne kaɗai zai kara tabbatar da irin laifin jami’an rundunar.
Kazalika dai har yanzu bayyana ko cewa al’amarin zai zamo na kalwa daya dama ruwa bane kan ko shi ma DPOn rundunar za bi sahunsu a garkame ka abunda aka kira rashin kula da kuma sanya ido kan jami’an sa.