Rundunar ‘yan sandan Kebbi sun gano Shanu 36 daga hannun Barayin Shanu A Zamfata, kamar yadda Garba Danjuma Kwamishinan ‘yan sanda ya tabbatar.
Danjuma ya shaidawa manema labarai a garin Birnin-Kebbi a ranar Lahadi cewa; wadansu daga cikin wanda ake zargi da sace Shanun an kama su, yayin da wadansu kuma suka tsere.
Ya tabbatar da cewa masu sanya ido na ‘yan sandan ne suka yi tafiya daga Kebbi zuwa Zamfara domin gano Shanun, bayan wadansu mutum biyu masu suna Abubakar Juli da Alhaji Ardo daga kauyen Asarara sun shigar da korafin sace Shanu 43 a ranar 10 ga watan Satumba.
Kwamishinan ya ce bayan gudanar da bincike mai zurfi ne, aka cafke wai masi suna Abubakar Umar da Attahiru Sani daga kauyen Daki Takwas a karamar hukumar Gumi a jihar Zamfara, inda aka same su da Shanu 36 na sata. Sai dai ya ce wadansu da ake zargi da sace Shanun sun tsere amma ‘yan sanda na ci gaba da bibiyarsu domin cafke su.