Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce fashewar iskar gas da ta afku a karamar hukumar Babura ta jihar ta raunata mutane bakwai tare da lalata shaguna 17 da gidaje biyar.kamar yadda DAILY POST ta ruwaito
Dimokuradiyya ta rawaito cewa fashewar iskar gas ta raunata mutane tare da lalata gidaje da shaguna a Babura a daren jiya Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masarautar Kano Zata Daura Damarar Neman Al’umma Su Mallaki Katin Dan Kasa
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu Adam, ya ce lamarin ya faru ne a daren jiya lokacin da jami’an hukumar kwastam da ke aikin sintiri a kan iyaka suka bi motar da ke dauke da gas din girki da ta taso daga Jamhuriyar Nijar zuwa Hadejia.
Ya bayyana cewa da isa mahadar biyu a garin Babura, bututun iskar gas din ya fashe.
Shiisu ya ce mutane bakwai ne suka jikkata sakamakon haka, sannan shaguna 17 da gidaje biyar sun lalace.
Ya ce an garzaya da wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gumel domin kula da lafiyarsu
A WANI LABARIN KUMA: An Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasar Kenya, Bayan Nasara A Zaben Kasar
Sabon shugaban kasar Kenya, Mr Willaim Samoei Ruto ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Kenya na Biyar.
Babban magatakardan ma’aikatar shari’a ne ya rantsar da sabon shugaban, yayin da taron daka gudanar yau, wanda ya samu halartar dubban mutane daga cikin da wajen kasar.