Da Dumi-Dumi: Yan sanda Sun Karbe Iko Da Majalissar Dokokin Jihar Ekiti
Wakilin DAILY POST da ya ziyarci harabar majalisar ya ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda na jibge a muhimman wurare a cikin harabar majalisar domin dakile duk wata barazanar tabarbarewar doka da oda.
An kuma hangi ma’aikatan majalisar na fitowa daga ofisoshinsu zuwa gidajensu.
A wata hira da wasu ma’aikatan da ba su so a ambaci sunayensu sun bayyana cewa akwai wani umarni daga hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti da ke neman ma’aikatan su fice daga harabar domin samar da zaman lafiya tare da bayyana cewa wasu mutane na shirin kai hari a majalisar. Majalisa.