By Abbas Yakubu Yaura
Wasu jami’an ‘yan sanda sun gudanar da zanga-zanga kan rugujewar da ake yi wa wani barikin ‘yan sanda na mutanen su a Miniokoro da ke karamar hukumar Obio/Akpor a jihar Ribas.
Daya daga cikin masu zanga-zangar da ba ya son a buga sunansa ya ce ba a sanar da jami’an yadda ya kamata ba kafin rugujewar.
“Ya zo mana da kaduwa. Muna cikin gidajenmu da safiyar (jiya) sai kawai muka ga buldoza tana rushe mana gidaje.
“Ba a sanar da mu ba kafin matakin. Zai shafi aikinmu, Iyalanmu sun riga sun yi gudun hijira. Muna kira ga mahukunta da sufeton ‘yan sanda da su taimaka mana wajen ceto lamarin,” kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.
Masu zanga-zangar dai sun samu shawara daga Paramount Ruler na Rumuobiakani al’ummar Rumuobiakani mai masaukin baki, Eze Temple Ejeku, da su kwantar da hankali tare da barin umarnin Sufeto Janar na ‘yan sanda ya ci gaba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ta ce ya samo asali ne daga matakin da rundunar ‘yan sandan ta dauka.
Koko tace, “Rundunar ta na sane da aikin rushewar.Wadannan mutanen ba bisa ka’ida suke ba, ba su da C of O, idan suna da su, sai su fito da shi.” Wannan fili na ‘yan sandan Najeriya ne, kuma ‘yan sanda suna lalata gidajen na bariki.
“Hukumomin ‘yan sandan sun amince da matakin ne saboda akwai wasu mutane a cikin barikin da suke da kokwanto akan su, don haka suka yanke shawarar rusa baraguzan gine-gine da haramtattun gine-gine a cikin bariki. Sake fasalin cikin gida ne ke gudana a cikin ‘yan sanda.”