Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wani matashi dan shekara 21, wanda ake zargin ya kashe mahaifinsa mai shekaru 70 a duniya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, a ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC Ta Sanya Ranar Da Za’a Gudanar Da Zaben Gwamna A Jihohi Uku
Hundeyin ya ce, rundunar ‘yan sanda da ke yankin Abule-Egba a jihar ta samu rahoton kisan ta bakin matar wanda aka hallaka, wanda kuma ita ce mahaifiyar wanda ake zargin a ranar Asabar.
“Mai karar ya kara da cewa a lokacin da ya isa babban asibitin Oke-Odo, likita ya tabbatar da rasuwar marigayin.”
“Yan sanda sun ziyarci wurin da aka aikata laifin, sannan an kai gawar zuwa dakin ajiye gawa na babban asibitin Isolo domin a tantance ta.
“An garzaya da wanda ake zargin zuwa sashin binciken laifuka na Panti na panti dake jihar domin gudanar da cikakken bincike,” inji shi.
A wani labarin kuma, Sauya Sheka: Jam’iyar PDP Ta Kusa Zama Tarihi A Jihar Sokoto– Wamakko
Jam’iyyar APC a jihar Sokoto, ta ce ta sake samun wasu jiga-jigan yan siyasa daga jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyar, gabanin babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai ba da shawara na musamman ga Aliyu Wamakko ya raba wa manema labarai ranar Talata a Sokoto.