By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an ‘yan sanda sun kama wani magidanci mai suna Soji Bakare mai shekaru 40 bisa zargin yi wa wata ‘yar makarantar firamare ‘yar shekara 10 fyade a dakin iyayenta dake Akure, babban birnin jihar Ondo.
An kama wadda ake zargin ne a lokacin da yake kai wa yarinyar hari a gidan iyayenta dake kan titin Aiyemi, unguwar Isolo a Akure, babban birnin jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa mahaifiyar yarinyar tana cikin kasuwa inda take siyar da kayan miya a lokacin da wanda ake zargin ya kutsa kai cikin gidansu inda ya afkawa diyarta ta.
Rahotannin sun bayyana cewa wanda ake zargin matarsa lokacin da abin ya faru itama tana wuri guda da mahaifiyar wanda aka yiwa fyaden inda ya nufi gidan iyayen wadda aka cutar bayan ya tabbatar da cewa mahaifiyarta ta bar gidan zuwa kasuwa.
Majiyar ‘yan sanda tace “wanda ake zargin ya bar gidan sa na Edo, Oke Ijebu Akure inda ya aikata laifin a lslo bayan ya lura cewa mahaifiyar yarinyar ta bar gida zuwa kasuwa.
“Da isarsa gidan sai ya yi amfani da yarinyar da mahaifiyarta ta bari ita kadai a gida.” Amma a lokacin da yake aikata laifin, sai wasu makwabtan ta da suka ji kukan wanda aka aikatawa laifin suka garzaya dakin suka kama wanda ake zargin.
Da take zantawa da manema labarai, mahaifiyar yarinyar,mai suna Yinka, tace Samariyawan kirki ne suka kama wanda ake zargin yana yi wa diyarta fyade a cikin dakinta sannan suka mika shi ga ‘yan sanda.Yinka tace jami’an ‘yan sanda sun garzaya da ‘yarta wani asibiti mai zaman kansa domin yi mata magani.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da cafke wanda ake zargin, inda ta kara da cewa nan ba da jimawa ba za a mika shi zuwa CID na jihar domin gudanar da cikakken bincike.Odunlami yace nan take za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu saboda girman laifin da ya aikata.
‘