A ci gaba da sauraran karan zaben shugaban kasa jam’ian ‘Yan Sanda zasu rufe hanyar goodluck ebele da shehu shagari Wanda sune suke kai mutum har zuwa kotun.
Mai magana da yawun ‘Yan sandan birnin tarayya DSP Anjugurimanzha a wata sanarwa da ya fitar ranar talata inda yace zasu kange manyan hanyoyin da zasu hada mutum zuwa kotun saboda samun tsaro yace anyi haka ne saboda kar wasu magoya bayan ‘Yan siyasa kar su tada wani hargitsi .
Ya shawarci mazauna yankin da subi wasu hanyoyin Dan samun sauki a yau larabar nan, in ji shi.