Yan Sandan Borno Sun Cafke Mutane 10 Wadanda Ake Zargi da Fashi Da Makami
Yan sandan Borno sun nasarar garkame wadanda ake zargi da Fashi da makami da kuma safarar miyagun kwayoyi a cikin jahar.
Wadanda ake zargin an taba kamasu a watan Aprilu 29 da kuma watan Mayu 28 a shekarar 2021 a garin Jos, Maiduguri, Kano, Yola, Abuja, Damaturu da kuma Jalingo a Jahar Taraba.
KARANTA:-Magatakardar jam’iyar APGA na kasa ya sauya sheka zuwa APC a Zamfara
Kwamishinan Yan Sanda Bello Makwashi yake sanar da Cafke su a ranar Litini, Ya Kara da cewa a watan Aprilu 29 misalin karfe 9 na yamma an kama Emmanuel Akachukwu da Isa Goni an kamasu a Kano kan laifin fashi a banki.
Kamar yadda ya bayyana su biyun sun shahara wajan fashi da damfara a tsakanin 15 zuwa 28 na watan Mayu wannan shekarar.
Edet Okon wakilin Makwashin yace da akwai wasu mutum biyar da aka Cafke suma a Jos da Jalingo da kuma Kano kan satar Miliyan 23.
Yace wadanda aka kama sun hada da Malam Hamisu, Umar Samaila, Habibu Garba, Ali Yahaya da Mari Paul.
Bayan a Cafke su, sun tabbatar da laifin su na satar Miliyan 23 a Sakateriya ta Musa Usman dake Maiduguri, sun kuma tabbatar da laifin su na fashi da makami a Kano, Jos, Maiduguri har da Zamfara da Jigawa.
Sannan an kamasu da kudade kimanin miliyan 14 da kiyakiyan mota guda biyar da kuma motoci biyar.