By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Delta sun kama wasu mutane shida da ake zargi da yin garkuwa da mutane da fashi da makami a sassan jihohin Delta da Bayelsa.
A cikin mutane shidan, an kama wasu mutane uku Godstime Rufus mai shekaru 22 da Stanley Efeme mai shekaru 21 da Davidson Esiso mai shekaru 35, dukkansu daga yankin Agbarho da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa a jihar, wadanda yanzu haka suna tsare a wajen ‘yan sanda.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar DSP Bright Edafe, ya fitar, ya ce an sace mutumin da lamarin ya rutsa dashi wanda (a sakaya sunansa) da karfe 9:30 na dare. ranar 22 ga watan Janairu, 2022, akusa da titin Esiso a Agbarho. An yi sa’a, ya tsere yayin da aka mayar da shi wata motar.
Sai dai daga baya wanda abin ya shafa ya hangi daya daga cikin wadanda suka sace shi mai suna Rufus sannan ya sanar da ‘yan sanda lamarin da ya kai ga cafke wadannan mutane ukun.
Kazalika an kama George Akporie mai shekaru 25 da Prosper Asaeta mai shekaru 29 da Ezekiel Stephen mai shekaru 23 daga yankin Igbide a karamar hukumar Isoko ta kudu a garin Sagbama dake jihar Bayelsa bisa laifin yiwa wani fashi.
Mutumin mai shekaru 33 wanda (aka sakaya sunansa) an yi zargin an harbe shi ne a ranar 5 ga watan Maris 2021, da wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi ne suka harbe shi kuma an sace masa babur dinsa na Qlink.
A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a tsakanin al’ummar Olomoro da Ehnwe da ke karamar hukumar Isoko ta Kudu daga bisani aka garzaya da wanda lamarin ya rutsa dashi zuwa babban asibitin Olomoro. inda aka yi masa magani aka sallame shi.
Sai dai kuma sa’ar ta kare daga ‘yan fashin ne a ranar 23 ga watan Janairun 2022, wanda abin ya shafa ya hangi daya daga cikin ‘yan fashin a kusa da Sagbama a jihar Bayelsa kuma nan take ya sanar da hukumar ‘yan sanda ta Bayelsa sannan aka dauko wadanda ake zargin.
Edafe ya bayyana cewa, an samu wata bindiga da aka kera a cikin gida daga hannun mutanen uku kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.