By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tace cafke wasu mutane biyu da ake zargi da satar saniya a karamar hukumar Garki da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Litinin a birnin Dutse.
Shiisu ya ce an kama wadanda ake zargin ne bayan wani Nasiru Magaji ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa a ranar 14 ga watan Disamba da misalin karfe 2:30 na dare wasu barayin da ba a san ko su wanene ba suka shiga gidansa suka sace masa saniya.
Ya bayyana cewa, bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda sun shiga aiki tukuru inda daga bisani suka kwato saniyar da aka sace inda aka kaita kasuwar Wudil dake jihar Kano don sayarwa.
Kakakin ya kara da cewa an kama mutanen biyu masu shekaru 30 da haihuwa da kuma mazauna kauyukan Jaya da Daware a karamar hukumar Garki dake Ringim.
A cewarsa, wasu mutane biyu da ake zargin mazauna kauyukan Jaya da Badage,a kananan hukumomin Garki da Ringim, har yanzu suna hannunsu.
Shiisu yace, za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike, yayin da ake ci gaba da kokarin zakulo mutanen biyu da suka gudu.