By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da yin barna tare da yin sata a wani kamfanin sadarwa da ke Ota, a karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta jihar.
Wadanda ake zargin, Kabiru Olusola, mai shekaru 27; Taye Daniel, 43; da Afeez Balogun, mai shekaru 47, an kama su ne biyo bayan kiran da jami’an ‘yan sandan da ke hedikwatar ‘yan sanda reshen Atan Ota suka samu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce babban jami’in tsaro na kamfanin mai kula da bargon, Shu’aib Muhammed, ya sanar da ‘yan sanda cewa wasu barayi kusan su shida ne suka kai farmaki inda abin ya faru dake Ketu kan titin Agbara.
Oyeyemi ya kara da cewa, biyo bayan kiran da jami’in ‘yan sandan yankin, Atan Ota suka samu ya aike da tawagar ‘yan sintiri zuwa wurin, inda aka damke mutanen uku, yayin da wasu suka tsere.
Ya ce, “Bayan an kai musu daukin gaggawa, DPO, sashin Atan-Ota, ya aika da tawagarsa da ke sintiri cikin gaggawa zuwa wurin, inda aka damke wadanda ake zargin uku, yayin da sauran suka tsere.
“An kwato daga hannun wadanda ake zargin akwai batura guda bakwai da kudinsu ya kai naira miliyan 3m, samfurin gyaran fuska, da kuma motar da suke aiki, mai lamba, AAA 779 XL.”
Oyeyemi ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin da nufin gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da wuri.
Ya kara da cewa CP din ya kuma bayar da umarnin a farauto ‘yan kungiyar da suka tsere domin gurfanar da su a gaban kuliya.