Amnesty International ta zargi ‘yan sandan Kenya da kashe mutane 167 ba bisa ka’ida ba a shekarar da ta gabata, ciki har da wasu daga cikin wadanda aka kama da laifin karya dokar Covid-19.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta yi zargin cewa rundunar na da alhakin kan bacewar mutane 33 a shekarar 2021.
A cikin rahotonta na duba abubuwan da suka faru a shekarar 2021, Amnesty ta zargi ‘yan sanda da yin amfani da “karfi mai wuce kima a wasu lokutan wajen wargaza masu zanga-zanga” kuma ta ce da yawa daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin ba sa fuskantar shari’a.
“An fara gabatar da kara 28 ne kawai a kan wadanda ake zargi da aikata kisan ba bisa ka’ida” kamar yadda kungiyar kare hakkin ta ce.
Kungiyar ta kuma yi nuni da wasu kararraki da suka hada da na Alex Macharia Wanjiku, wanda aka harbe shi a gundumar Nairobi lokacin da aka ce jami’an tsaron kasar Kenya, sun yi kokarin tarwatsa wata zanga-zangar adawa da hukumar kula da harkokin sufuri da lafiya da ci gaban birnin.
Rahoton ya ce “Ba a kammala binciken da hukumar sa ido kan harkokin ‘yan sandan kasar ta IPOA ta fara ba,” in ji rahoton.
Har yanzu dai ‘yan sandan Kenya ba su ce uffan ba kan rahoton na Amnesty.
A baya shugaban kasar ya ba da uzuri game da zargin ‘yan sanda da ake zargi da ” wuce gona da iri’ lokacin tabbatar da dokokin dakile yaduwar cutar Covid-19.
Ana yawan zargin ‘yan sandan kasar da ke gabashin Afirka da aikata ta’asa, amma, gwamnatin kasar ta Kenya ta ce, jami’anta suna da horo sosai