By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas dake binciken manyan laifuka, Panti,tace ta kama wasu mutane 12 da ake zargi da hannu a kisan dan sanda Kazeem Abonde, babban Sufeton ‘yan sanda.
Marigayi Abonde, wanda tsohon jami’in gudanarwa ne na rundunar ‘yan sandan, an kashe shi ne a ranar 23 ga watan Satumba a wani samame da aka kai maboyar ‘yan ta’adda a Estate Ajao dake Legas.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, CSP Adekunle Ajisebutu ya sanyawa hannu kuma aka fitar ranar Talata a Legas, tace an kama wadanda ake zargin ne bayan an gudanar da bincike mai zurfi.
Sannan an kama wani mai suna Ismaila Abdullahi Haruna mai shekaru 23 da kuma wasu mutum 11 da ake zargi da hannu a wani gagarumin bincike na tsawon makonni hudu da jami’an ‘yan sanda suka gudanar.
“Wadanda ake zargin tuni suka amsa laifukan hadin kai, kisan kai, yunkurin kisan kai da kuma lalata da gangan an kama su ne a maboyarsu dake jihohin Legas da Nasarawa inda suke yin hidimomi don gujewa kama su bayan sun aikata wannan aika-aika.
“Lokacin da ake yi masa tambayoyi, wadanda ake zargin sun ba da labarin yadda aka kai mummunan harin da aka kai wa dan sandan daya yi sanadiyyar mutuwarsa da sauran jami’an ’yan sandan da suka jikkata da kuma ayyukan aikata laifuka kowanne.
Kazalika jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Sahihan bayanan sirri da suka samu yasa aka kama su.”Sai dai CSP Ajisebutu, ya kara da cewa za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotun Majistare ta Yaba a ranar Laraba.
kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, CP Hakeem Odumosu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya raba wa manema labarai a ranar Asabar inda yace sun sha alwashin kama duk wadanda ake zargi da hannu a harin da aka kai wa ‘yan sandan.