Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi, CP Umar Mamman Sanda, ya ce rundunar ta ceto mutane biyu daga hannun masu garkuwa da mutane a dajin Alkaleri.
A ranar Lahadi 31 ga watan Yuli ne tawagar ‘yan sintiri da ke sashin Alkaleri, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na Danga dake aikin ceto suka kai samame a ranar Lahadi 31 ga watan Yulin shekarar nan.
Kwamishinan ya ce sun ci karo da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne dauke da bindigu sannan suka yi artabu tare da samun nasarar ceto biyu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su mai suna Adamu Alhaji Usman mai shekaru 19 da Sahura Alhaji Sunusi mace mai shekaru 17 a kauyen Garin Bakwai da ke unguwar Maimadi tare da kwato babura hudu daga hannun masu garkuwa da mutanen.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ku taimaka mana wajen magance matsalar tsaro – Shugaba Buhari ga kasashen duniya
DAILY POST ta ruwaito cewa an kai wadanda aka kubutar da su asibiti domin kula da lafiyarsu yayin da guda daga cikin masu garkuwan ya tsere da munanan raunukan da ya samu a harbe-haren.
A wani labarin kuma na daban.
Yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sake sakin wasu fasinjoji 5 da suka yi garkuwa da su a yau Talata.
Mutane 5 da abin ya shafa su ne Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal; Abubakar Ahmed Rufa’i Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.
Yayin da yake tabbatar da sakin su ga manema labarai a Kaduna, jagoran sasantawa kuma mai ba wa Sheikh Ahmad Gumi shawara kan harkokin yada labarai; Malam Tukur Mamu ya ce kamata ya yi gwamnati ta gaggauta yin shawarwari domin ganin an sako sauran wadanda aka yi garkuwa da su domin suna cikin hadari.
Ya kuma yi kakkausar suka masu cewa tattaunawa bata da amfani, inda hakan akwai muhimmanci a ciki sosai wato tattaunawa da ‘yan ta’adda, yana mai jaddada bukatar hakan.
“A yanayin da rundunar soji ba za ta iya aiki ba, tabbas tattaunawa za ta yi aiki,” in ji shi.
Dukkanin wadanda aka sako kwanan nan sun mika godiyarsu ga Allah tare da godewa Tukur Mamu bisa rawar da ya taka yayin tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da su.