Rundunar Yan sandan jihar Filato ta dakile yunkirin masu Garkuwa da mutane, na kai hari a garin Rantya dake karamar hukumar Jos ta Kudu, a yammacin jiya Asabar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Ubah Ogaba ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar, inda ya ce, rundunar tasami sanarwar sirri ta hanyan Kiran waya salula na yunkurin harin yan bindigan a garin.
A cewar shi, “A jiya Asabar da musalin karfe 3 na yammaci, Mun sami labarin cewa, yan bindiga sun afka garin Rantya, domin su yi garkuwa da wani Mutum, da kuma wasu mutane a yankin” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina so Inyi aure Amma ban samu kalar mijin da na keso ba, inji Amaryar kamaye
Ogaba ya kara da cewa, jami’an yan sanda sun yi nasarar kashe guda daga cikin masu Garkuwa da mutanen, ya yin da wasu daga cikin su, suka tsira da raunikan harbin bindiga, sakamakon musayan wuta da bangarorin biyu suka yi.
Kazalika ya ce, tuni a ka fara gudanar da bincike, kuma rundunar yan sandan sun fara bi-bi-yan yan bindigan.
Wannan na zuwa ne, ya yin da Jihar Filatoi ke ci gaba da fama da hare-hare yan bindiga, a yan kwanakin nan.