Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta ce an sako mawakin nan, Oluwatobiloba Anidugbe, wanda aka fi sani da Kizz Daniel, daga hannun ‘yan sanda a Tanzaniya.
Wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta a ranar Litinin ya nuna lokacin da hukumomin Tanzaniya suka kama mawakin.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance, amma jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa, kamun ba zai rasa nasaba da gazawar mawakin ba a wani biki da aka gudanar a kasar, wanda kuma anan ne ake zargin ya aikata ba daidai ba.
Katsina: Yan Gudun Hijira 12,000 Sunyi Nasarar Komawa Matsugunansu na Asali
Da take mayar da martani, hukumar NiDCOM, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa ana tsare da mawakin ne a ofishin ‘yan sandan farin kaya na Oyster Bay da ke Dar es Salaam, Tanzania.
Da take karin haske kan wannan batu, NiDCOM ta ce, “An saki Kizz Daniel.
Tawagar lauyoyinsa za ta kai rahoto ga ‘yan sandan kasar a gobe, sannan kuma daga bisani zai dawo Najeriya.”