By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaron ‘yan sanda a jihar Zamfara sun cafke wani kasurgumin dan bindiga da aka fi sani da Maiyammata a ranar Laraba.
An kama mai laifin ne a karamar hukumar Zurmi dake jihar Zamfara a lokacin da yake sintiri a yankin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, yace an kama shi ne a lokacin da yake kokarin yin garkuwa da wasu fasinjoji a kauyen Koliya.
Maiyammata, wanda tsohon dan kungiyar Bello Turji ne, yanzu ana kyautata zaton yana aiki ne da wani basarake da ake nema ruwa a jallo mai suna Kachalla Sani-Black.
Sani-Black wanda ya kasance yana gudanar da aikin sa ne a kananan hukumomin Zurmi, Shinkafi, da Birnin Magaji a jihar.
Sannan yace an kwato “Bindiga AK-47 guda daya, albarushai guda biyu tare da harsashi guda uku, da kuma babur Boxer daya a wajen sa,” in ji CP.
Elkanah ya kara da cewa ana kokarin cafke wadanda ke da hannu da rikicin Maiyammata kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.