Mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a sun yi Allah-wadai da gwamnatin tarayya bisa gazawarsu na sakin shugabansu, Sheikh Ibraheem Zakzaky da matarsa shekaru hudu bayan da wata babbar kotu a Abuja ta ce a sake su.
‘Yan Harkar Musuluncin sun bayyana hakan ne cikin sanarwar da shugaban Resource Forum, Farfesa Abdullahi Danladi ya rabawa manema labarai a ranar Asabar, inda ya ce kin bin umurnin hukuncin da Alkali Gabriel Kolawole ya yanke na a saki Shaikh Zakzaky da matarsa cikin kwana 45 wanda yau tsawon shekaru hudu ke nan, shi ne mafi munin take hakkin bil’adama na ma’auratan da take dokokin kasa da gwamnatin ta yi.
“a yau muna tunawa da shekaru hudu na karewar wa’adin kwanaki 45 da aka bai wa gwamnatin Buhari ta saki Sheikh Ibraheem Zakzaky sakamakon hukuncin nan mai dimbin tarihi da Alkali Gabriel Kolawole na Babbar kotun Abuja ya yanke kan ‘yancin Sheikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenah Ibrahim”, inji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa; “rashin bin umurnin kotun da shugaba Muhammadu Buhari ya yi shekaru hudu bayan hukuncin, kuma har yanzu bai bi ba, ya sanya shi cikin jerin mafi munin take doka da take ‘yancin bil’adama da aka yi”, ya tabbatar.
Farfesa Danladi ya ce; Alkalin ya yanke hukuncin cewa; ci gaba da tsare su take ‘yancinsu ne kuma ya sabawa sashe na 35 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma dokokin kare hakkin bil’adama na Afrika. Inda suka ce abin takaici ne rashin bin wannan umurnin na sakin su da kuma ba su muhallin da za su zauna kamar yadda kotun ta nema.
“har wala yau kotun ta ce gwamnatin tarayya ta biya su diyyar naira miliyan 50 ga Sheikh Zakzaky da matarsa bisa take ‘yancinsu”, suka lurantar.
Ya kara da cewa; Alkali Gabriel Kolawole ya ce ci gaba da tsare El-Zakzaky da matarsa daga gwamnati ya sabawa doka. Inda ya ce babu wata doka a kasarnan da ya bai wa hukumomi damar ci gaba da tsare mutum ba bisa ka’ida ba. “Alkalin ya gargadi gwamnati a cikin hukuncin da cewa ci gaba da rike Shehin Malamin babbar barazana ne, inda ya jaddada cewa; idan Sheikh Zakzaky ya mutu a wurin da ake ci gaba da tsare shi, wanda ba ni fatan hakan (inji Alkali), hakan zai janyo asarar rayuka daban-daban”. Ya nusasshe.
Farfesa Danladi ya ce amma gwamnati ta zama tamkar kurma tana ci gaba da tsare Shehin Malamin maimaikon su sake shi, inda suka koma suna yi wa Shehin Malamin zargi marasa tushe ta hannun gwamnatin Kaduna.
“rashin girmama umurnin kotu daga gwamanti yunkuri ne na haddasa rikici kamar yadda wani Farfesan sanin dokoki ya ce a daidai lokacin da aka ce ana kan turbar dimokuradiyya. Kafin a kai ga daukar wani mataki na sakin wani mutum ko bada belinsa, gwamnati na duba ga muhawarorin wanda ake zargi da gwamnati. A don haka baa bin a amince bane gwamanti ta rika zabar umurnin da za ta bi da wanda ba za ta bi ba”, inji shi.
“abin godiya ga Allah ne a ce shekaru hudu bayan da kotu ta bada umurnin a Saki Shaikh Zakzaky da matarsa, amma bamu taba kasa a guiwa ba wajen neman ganin an sake su ba bisa sharadi ba”.
“kungiyoyi da dama na kasashen waje ciki harda Amnesty International da kungiyar Tarayyar Turai duk sun bai wa gwamnatin Nijeriya shawarar bin dokoki wajen sakin Shehin Malamin. Za mu kuma ci gaba da yi ba tare da la’akari da matakin karfi da gwamnati ke ci gaba da amfani da shi ba”. Ya tabbatar.
A karshe ya karkare da cewa; ba za su taba kasa a guiwa ba wajen ci gaba da neman ganin an saki Shehin Malamin na su, inda ya ce za su ci gaba da bin duk wata hanyar da ta dace wajen hakan. “a don haka muna sake kira da a saki Shehin Malamin da matarsa ba tare da wani sharadi ba, da duk wanda ake ci gaba da tsarewa tun kisan kiyashin Zariya da sojojin Nijeriya suka yi a watan Disambar 2015”, inji shi.