Tsohon Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, Alhaji Abubakar Tsav ya ce mafi yawan ‘yan siyasan Nijeriya ba su yi Imani da Allah ba.
Tsav ya bayyana haka ne a cikin wata takardar manema labarai da ya fitar a ranar Talata a garin Makurdi.
“Yan siyasarmu ba su yi Imani da Allah ba, kuma bas u yarda duniya ba komai ba ce. Ba sa tunanin mutuwa.
Dimokuradiyyarmu ta dauko hanyar lalacewa. Bamu ma san menene dimokuradiyya ba. Da dama kallonta suke a matsayin hanyar samun kudin haram,” inji Tsav.
Ya ce, har sai kotu ta fara daure mutanen da aka kama da zargin rashawa don ya zama darasi ga na baya, jami’an gwamnati za su daina rashawa. Ci gaba da kushe jami’an babu hukunci ba zai tsayar da rashawa a kasar nan ba.