Rundunar Sojin Najeriya ta haɗa hannu da yan sanda inda suka yi nasarar hallaka yan ta’adda a Karamar Hukumar Essien Udim dake Jihar Akwa-Ibom.
Wadannan yan bindiga sun maida wurin ya zama tamkar matattarar yaki sakamakon irin hare-hare da suke kaiwa ba dare ba rana.
A cewar Kakakin Rundunar Sojin Birgediya Janar Muhammad Yarima, cikin aika-aikar yan ta’addan a baya sun yi nasarar hallaka Jami’in ɗan Sanda guda tare da awun gaba da makamin sa.
Ya ce wannan ne ya sa rundunar sojin ta yi fargar jaji tare da tashi tsaye ta haɗa hannu da yan sandan don Maido da doka da oda a yankin.
“Abubuwa a Akwa-Ibom na tafiya daidai yadda ya kamata, to amma wasu marasa kunya sun zo suna son tada hankalin jama’a”
“Makonni da suka gabata yan ta’addan sun yi ta kai farmaki ga jami’an tsaro inda har ya kai ga asarar rayuka tare da kwace makaman su”
“Haka yan ta’addan suke ta ci gaba da kai komo a yankin suna tada hankalin bayin Allah” cewar Kakakin Rundunar sojin.