Hedikwatar tsaro ta ce ‘yan ta’adda 4,770 da suka kunshi maza 864 da mata 1,415 da kananan yara 2,490 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya tsakanin 1 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuni a yankin Arewa maso Gabas.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na ma’aikatar tsaron ta kasa Manjo Janar Bernard Onyeuko, ya bayyana haka ne a taron manema labarai na mako-mako kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis, a Abuja.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Onyeuko ya ce sojojin na Operation Hadin Kai sun kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu a wurare daban-daban na shiyyar Arewa maso Gabas.
Ya kuma kara da cewa ayyukan sun kai ga ceto mutanen da aka sace, da kawar da ‘yan ta’adda, kame ‘yan ta’adda, kwato makamai da alburusai da sauran abubuwan da suka shafi tsaro.
Onyeuko ya ce sojojin na bataliya ta 152 a tsakanin 17 ga watan Yuni zuwa 21 ga watan Yuni sun yi arangama da mayakan Boko Haram da ke gudun hijira a garin Buduwa dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Kazalika Ya kara da cewa an kwato shanu 14 da aka sace da kuma kekuna uku tare da kama wasu masu hada kai da ‘yan ta’adda da kuma masu samar da kayayyaki ga masu tada kayar bayan.
A cewarsa, an kama Malam Abacha Usman a Benshek, Malam Ibrahim Gira da ke kan titin Damboa – Biu da kuma Malam Ibrahim Gira – wani dan ta’adda mai samar da man fetur.
Ya ce, sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 11, sun kama 11 tare da kwato shanu 14, bindigogi kirar AK47 guda biyu, kekuna uku, bindigogin gida guda biyu, harsashi 90 na 7.62mm, da mota kirar Golf 2 guda daya.
“Dukkan ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP da iyalansu da suka mika kansu an ba su bayanan sirri da iyalai yayin da aka mika su ga hukumar da ta dace domin daukar mataki,” in ji shi.