By Ishaq Dabai
Hedkwatar tsaro ta soji tace ya zuwa yanzu ‘yan ta’adda 13,243 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a Arewa maso Gabas.
Mukaddashin Darakta, Ayyukan Kafafen Yada Labarai na Tsaro, Brig.-Gen. Bernard Onyeuko, shine ya bayyana hakan yayin da yake ba da bayanai kan ayyukan soji a fadin kasar a ranar Alhamis a Abuja.A cewar Onyeuko, ‘yan ta’addan da suka mika wuya sun hada da maza 3,243, mata 3,868 da kuma yara 6,234.
Onyeuko ya kara da cewa sojojin da suke aiki Hadin Kai sun ci gaba da kasancewa cikin matsanancin hali tare da karfin gwiwa a Arewa maso Gabas, wanda ya ba da sakamako mai mahimmanci a cikin makonni biyu da suka gabata.sannan yace jerin ayyukan kasa da na sama da aka gudanar a wurare daban -daban na Arewa maso Gabas ya rage karfin ayyukan maharan tare da kashe yawancin su.
Kazalika Onyeuko yace an kama wasu da dama tare da masu bada labarai da masu samar da kayan aiki, yayin da wasu ‘yan ta’adda suka ci gaba da ajiye makamansu da mika wuya ga sojojin tare da iyalansu.“Wasu daga cikin wadannan abubuwan an da aka tattara an samesu a hanyar Gwoza – Yamtake-Bita, Gwoza – Farm Center – Yamtake, da yankin tsaunin Mandara da Pulka da Hambagda, duk a jihar Borno.
“Bugu da kari, an kwato tarin makamai 38 da harsasai daban -daban 968 da kuma dabbobi 48 da aka sace tare da wasu abubuwa da dama.”Zuwa yanzu, jimlar ‘yan ta’adda 13,243 da iyalansu da suka kunshi maza 3,243, mata 3,868 da kuma yara 6,234, sun mika wuya ga sojoji a wurare daban -daban a Arewa maso Gabas,” in ji shi.
Onyeuko ya bayyana cewa Rundunar Sojin Sama ta Operation Hadin Kai ta kai hare -hare ta sama don dakile harin ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da ‘yan ta’addan suka kai wa sansanin sojojin kasa a kauyen Aulari a yankin Bama na Borno.