A jiya ne da misalin karfe shida na yammaci, ‘Yan ta’addan barayin shanu dauke da muggan makamai suka shiga garin wagini da garin Daurawa da ke Karamar Hukumar Batsari a jihar Katsina, Inda suka rika harbi ba kakkautawa.
‘Yan bindigar sun jikkata mutane da dama daga ciki har da jami’an tsaron soja guda uku sannan suka kone motar sojojin guda uku Kuma suka kwance babbar bindigar da ke kan motocin suka tafi dasu.
Yanzu haka al’amurrah suna cigaba da rincabewa inda mazauna kauyukan suke ta tserewa domin tsira da rayuwarsu.