Wasu gungun ‘yan bindiga guda biyu na shirin kai hare-hare a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da kuma Kudu maso Yamma, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga hukumar tsaro ta NSCDC ta bayyana.
Takardar wacce aka aika zuwa ga dukkan kwamandojin NSCDC mai kwanan wata 25 ga watan Yuli da wakilin Jaridar Daily Trust ya gani a jiya ya bayyana jihohin Legas da Katsina da Zamfara da Kaduna da Kogi da kuma babban birnin tarayya Abuja a matsayin wuraren da za’a kai hari.
Takardar ta samu sa hannun mataimakin kwamandan hukumar D.D. Mungadi
“Saboda haka, Babban Kwamandan ya umarce ku da ku kara kai kaimi a duk wurare masu mahimmanci, gami da makarantu, wuraren ibada da muhimman kadarorin kasa a jihohin ku, don bincikar duk wata barazanar da wadannan masu aikata laifuka ke yi. Da fatan za a kula da shi a matsayin sanarwar gaggawa, ”in ji bayanin.
KARANTA WANNNA LABARIN: Tinubu Ta Gana Da Wasu Gwamnoni, Da Masu Ruwa Da Tsaki A Abuja
A cikin sanarwar, hukumar NSCDC ta ce ta samu sahihin bayanan sirri da ke nuna cewa ‘yan ta’addar Boko Haram da kungiyar IS sun hada mayakansu tare da tura manyan makamai kamar bindigogin kakkabo jiragen sama, manyan bindigogi masu sarrafa kansu da dai sauransu domin kai hari jihar Katsina.
Sai dai kakakin hukumar NSCDC, Shola Odumosu, da aka tuntube shi, ya shaida wa wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa rahoton da aka fallasa ba daga hukumar ya fito ba.
“Babu wata sanarwa game da hakan,” in ji shi.
A halin da ake ciki, Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, a jiya, ya bukaci mazauna Abuja da su ba jami’an sa na hukumar leken asiri hadin kai domin karfafa rundunar FCT da zatai yaki da ‘yan ta’adda.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, IGP ya fitar, ya ce an bukaci hukumar leken asiri ta FIB da hada kai da mazauna yankin domin kakkabe abokan gaba da ke barazanar durkusar da kasar nan.
“IGP ya ba da umarnin tura wasu kadarorin zuwa wurare masu mahimmanci na Abuja yayin da aka bukaci Hukumar Leken Asiri kan tattara bayanan sirri da musayar bayanai tsakanin sauran hukumomin tsaro