‘Yan bindiga dauke da makamai sun tashi garuruwa sama da 70 a jihar Sokoto da ke Najeriya, yayin da suka kashe mutane da dama tare da sace musu dukiya da suka hada da dabbobi.
Bayanai sun ce akasarin mazauna garuruwan da maharan suka afkawa sun samu mafaka a manyan garuruwa, domin tsira da rayuwarsu.
Yayin da yake yiwa sashin Hausa na RFI Karin bayani Sanata Ibrahim Gobir dake wakiltar yankin, ya ce tashin hankalin ya shafi Rabah, Goronyo, sai kuma Isa, da Sabon Birni.
Sanatan ya koka bisa yadda har yanzu al’ummar yankin ke ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren ‘yan bindigar.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa a ranar 12 ga watan Yunin da ya gabata, rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar mutuwar mutane 8, sakamakon arangamar da aka yi tsakanin wani gungun ‘yan bindiga da jami’an tsaron sa akai na Vigilante a karamar hukumar Isa.