Kungiyar agaji ta kasar Norway ta ce ‘Yan ta’adda a Burkina Faso sun hallaka mutane akalla 480 tsakanin watan Mayu zuwa Agustan wannan shekara.
Kungiyar agajin ta bayyana damuwa dangane da karuwar yawan mutanen dake mutuwa da kuma rasa matsugunan su a watannin da suka gabata, ganin yadda aka tilastawa mutane sama da dubu 275 tserewa daga matsugunan su domin tsira da rayukan su tun daga watan Afrilun da ya gabata.
Alkaluman kungiyar sun nuna cewar akalla mutane dubu 55 ake rabuwa da matsugunan su kowanne wata, abin da ke nuna yadda adadin ya ninka har sau 3 sabanin yadda aka gani tsakanin watan Oktobar shekarar 2020 zuwa Maris din shekarar 2021.
Rahotan kungiyar yace alkaluman ta ya nuna cewar mutane sama da miliyan guda da dubu 400 suka tsere daga gidajen su domin kaucewa hare haren.
Kungiyar ta ce tsaikon da ake samu wajen kaiwa jama’a dauki domin basu kayan jinkai na tilastawa mutane zabi tsakanin matsalar tsaro da kuma yunwa.
Comments 1