- Yan ta’adda sun sace masu kiwon kaji guda biyu da wani a wurare daban-daban a ranar Laraba a Kogi
- Masu ruwa da tsakin a yankin sun bukaci a rika shigo da yan asalin yankunan domin samar masu da tsaro
- Wani dan asalin yankin da lamarin ya faru ya bayyana bakin cikinsa na yadda yan ta’adda suka mamaye dukkanin dazuzzukan dake yankunan da suke makwabta dasu
Yan ta’adda sun sace masu kiwon kaji da wani mutum, a Egbeda dake Kabba a shiyyar Kogi ta yamma, inda aka sace su a wurare daban-daban na jahar a ranar Laraba.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, biyu daga cikin wadanda aka sacen sun hada da; Olorunpomi Damilola, Ma’aikaci a Kwalejin Ilmi ta Fasaha ta Gwamnatin Tarayya dake Kabba, da Fasto Mayowa Otitolaye wanda dukkanin su, sun kasance masu kiwon kaji, a yayinda na ukun har yanzu ba’a san kowa ne ne shi ba.
Haka zalika, yan ta’adda sunyi harbi ne babu kakkautawa, domin tsoratar da al’umma a sa’ilin da suka sace mutanen da lamarin ya rutsa dasu a bayan Majami’ar Christ Apostolic a Egbeda-Kabba, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Shugaban Hukumar EFCC ya yanke jiki ya fadi a Aso Rock
Wani wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya yi nuni dacewa akwai bukatar dake akwai na shigo da aikin masu tsaro na yankin, domin taimakawa wajen kawo tsaro a al’ummomin, amma ya bayyana rashin jindadi akan rashin wayarwa al’umma akan hakan.
Yace amma wasu al’ummomi da suke makwabtaka dasu a Okun, sun dauki irin wannan matakin, domin magance irin wannan rashin tsaron al’umma da dukiyoyin su, inda ya jaddada bukatar dake akwai na yin irin wannan a fadin Kaba, domin bata gari da dama suna can sun cika dazuzzukan yankin.
Wani Yomi Obalore ya bayyana cewa dukkanin fadin Ikowaopa na Kabba na karkashin ikon wasu wanda ba yan asalin yankin ba, kuma akwai bukatar na kowa ya kaura daga wurin.
Mai magana da yawun Rundunar Yansanda DSP William Aya wanda ya tabbatar da lamarin, yace Babban Jami’i mai kula da yankin ya sanar da hedikwatar Rundunar da misalin karfe 9 na dare a ranar Laraba, kuma tuni tawagar jami’an rundunar da yan kungiyar sintiri, gami da sauran jami’an tsaro domin gano masu garkuwa da mutanen.
“Mutanen mu yanzu haka sun shiga dajin, kuma muna farin cikin sanar dacewa, yanzu haka za’a ceto wadanda akayi garkuwa da su gami da kama wadanda suka aikata garkuwa da mutanen,”inji Aya