Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wasu mata biyu da wani mutum a kusa da otal din Niger Motel da ke unguwar Jepap a garin Suleja na jihar Neja.
Yan bindigar sun yi garkuwa da mutane hudu ciki har da wata limamin coci a yankin tare da wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu da aka biya wa wadanda suka sace su a matsayin kudin fansa kafin su samu ‘yanci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kasar China Ta Kaddamar Da Gina Cibiyar Nazari A Birnin Tarayya
Wata majiya a unguwar ta shaidawa DAILY POST cewa masu garkuwan sun mamaye al’ummar ne da misalin karfe 1:00 na rana a ranar Asabar, inda aka yi garkuwa da wata matar aure da diyarta ‘yar shekara 18 a lokacin da suka shiga gidan.
Ya bayyana cewa kafin faruwar lamarin, uwar gidan ta samu rashin fahimtar juna da wani mutum, wanda ya yi barazanar cewa ta yi tsammanin martaninsa.
DSP Wasiu Abiodun, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, bai amsa kiran waya domin tabbatar da faruwar lamarin ba.
A WANI LABARIN KUMA: Jiragen Yakin Habasha Sun Tarwatsa Motar MDD
Ana cigaba da samun tashe tashen hankula a yaken Tigray bayan da wani harin da jiragen yaki marasa matuki suka kai a yankin dake arewacin Habasha ya afkawa wata motar hukumar abinci ta amajalissar dinkin duniya dauke da kayan agaji tare da raunata direban motar, kamar yadda mai magana da yawun hukumar samar da abinci na majalissar ya bayyana a ranar Litinin.
Hukumar samar da abinci ta duniya wata hukuma ce ta Majalisar Dinkin Duniya da ke taimakawa wajen samarda kayayyakin agajin jin kai zuwa yankin Tigray, inda aka shafe kusan shekaru biyu ana rikicin kuma ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da yin barna ga miliyoyin mutane