Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kawai zai yi wa yakin neman zabe a zaben shekarar 2023. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
A cewar Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, Buhari ba zai amince da tsaffin ‘yan jam’iyyar ko ‘yan siyasa da ke da shari’a a kotu a ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
KATANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Ba Mu Rena Karsashin PDP, Da APC Ba, Amma Jam’iyar NNPP Zata Bada Mamaki—–Kwankwaso
“Fadar shugaban kasa na son sanya shi a rubuce, kuma a lokaci guda, ta tabbatar wa ‘yan jam’iyyar masu aminci cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance mamba mai ladabi ga jam’iyyar All Progressives Congress, APC”
Gwamnatin Tarayya Tayi Ƙarin Girma ga Jami’an Kashe Gobara 2,382
Ya kara da cewa, “Wannan gargadine ga ‘yan jam’iyyar da suka sauya sheka da kuma wasu da har yanzu suke gaban kotu a kan zama dan takarar jam’iyyar APC cewa su na ma kan su ne kuma babu wanda ke wajen jam’iyyar da ya isa ya danganta abin da suke yi da Shugaba Buhari.”.