Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki da za a gudanar a mako mai zuwa wato a ranar Lahadi mai zuwa, a halin yanzu dai masu neman tikitin takarar kujerar shugaban kasa na yankin Kudu maso Gabas na gudanar da wata ganawar sirri.
na sirri wanda ke gudana a gidan sirri na tsohon gwamnan jihar Imo a Abuja, Rochas Okorocha, an fara shi ne da misalin karfe 3:45 na rana.
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana Makasudin taron ba, amma wani mai taimaka wa Okorocha da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa cewa taron ya ta’allaka ne kan yadda za a zabi dan takarar da ya dace a shiyyar.
“Yankin Kudu maso gabas da gaske yake wajen samar da shugaban kasa a wannan karon, wannan ya sa shugabanninmu suka kira wannan taro domin a samu maslaha.
Ina mai tabbatar muku da cewa shiyyar za ta tabbatar ta samar da jajirtacce cikin yan takarar wanda ya samu karbuwa a kasa baki daya,” in ji mataimakin.
Wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba; wani tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani; Okorocha da mace daya tilo mai neman takara, Uju Ohanenye.
Kamar yadda yake gabatar da wannan rahoto, gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, wanda shi ma ke neman kujerar kuma ake sa ran halartar taron, bai iso ba.
Comments 3