A yau Talata ne Allah Ya yi wa Shugaban Kasar Chadi Idriss Deby Itno rasuwa yayin wata arangama da yan tawaye a Kasar, kamar yadda Dakarun Sojin Kasar suka bayyana.
Mutuwar ta Mista Itno na zuwa Jim kaɗan baya sake zabar sa karo na shida kan karagar mulki.
A yanzu haka Sojin Kasar za su ci gaba da gudanar da mulkin kasar na tsawon watanni goma aha takwas bayan suka rusa gwamnati tare da majalisar kasar.
A shekarar 1990 ne dai Mista Itno ya hau kan karagar mulkin kasar bayan wani tawaye da aka nuna wa gwamnatin wanchan lokacin.
Tun a karshen mako ne dai tsohon Shugaban kasar ya jagoranci zuwa gurin da dakarun sojin kasar ke yaƙi da yan tawaye.