Mayakan tawaye na yanki Tigray dake kasar Habasha sun sake kwace iko da birnin Mekelle na kasar, lamarin da ya tilasta wa jami’an tsaro tserewa daga birnin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ana can ana murna baki har kunne yayin da dubban mutane ke ɗaga tutoci.
A yanzu haka gwamnatin kasar da ta kwace iko da birnin na Mekelle a watan Nuwamba bayan da yan tawayen Tigray din sun juya baya wa Kudirin maido da mulkin dimokuradiyya a kasar.
Wannan lamari dai ya janyo mutuwar dubban mutane yayin da sama 350, 000 suka rasa abinci.
Kawo yanzu mutane sama da miliyan biyu ne suka rasa Matsuguninsu sakamakon wannan tashe tashen hankula.