Yan tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun janye daga yankunan da suka kwace a baya-bayan nan biyo bayan kaurewar Wani kazamin fada tsakanin su da dakarun gwamnati a lardin Kivu dake Arewacin kasar.
Fadan dai ya raba mutane fiye da 100,000 da muhallansu a lardin, sai dai kafofin yada labaran kasar sun ce yanzu haka mazauna yankin da dama na komawa gidajensu a yankunan Rutshuru da Nyagongo.
Mai magana da yawun ‘yan tawayen M23, Manjo Willy Ngoma, ya shaidawa kafar yada labarai ta BBC World cewa “sun bar wadannan yankuna ne domin a samar da zaman lafiya”.
‘Yan tawayen sun bar lardin ne da kimanin tazarar kilomita 20 daga Goma babban birnin lardin.
Sai dai ba a san inda suka koma ba, amma gidan rediyo Okapi da Majalisar Dinkin Duniya ke daukar nauyinsa ya ce sun je wasu wurare da ke kusa da kan iyakar kasar DR Congo da Rwanda.
A ranar litinin mai magana da yawun gwamnati Patrick Muyaya ya yi watsi da yiwuwar tattaunawa da ‘yan tawayen, yana mai bayyana su a matsayin yan ta’adda.
Yace babu sauran damar tattaunawa da yan ta’adda a halin yanzu.
Sai dai kakakin ‘yan tawayen ya ce ayyana kungiyar ta M23 a matsayin kungiyar ta’addanci ba a bu ba ne dake kan tsari..
Gidan rediyon Rayhaan ya ruwaito cewa, a watan Afrilu gwamnatin Kongo ta cire kungiyar ta M23 daga tattaunawar da aka gudanar a Kenya tare da kungiyoyin ‘yan tawaye da dama, inda ta zargi kungiyar da tayar da kayar baya gabanin tattaunawar.
Tattaunawar dai ba ta kai ga cimma matsaya ba, kuma za a ci gaba da zama a lardin Goma domin lalubo hanyar warware rikicin.