Dakarun kabilar Tigrai sun ce sun janye daga yankunan yankin Amhara na kasar Habasha da suka mamaye sama da wata guda a cikin yakin basasar da ake ci gaba da gwabzawa a arewacin kasar Habasha.
BBC ta ruwaito cewa, A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na yankin, ‘yan kabilar Tigrai sun ce sun sake yin la’akari da tura Dakarun su saboda akwai bukatar yin sauye-sauye domin yakar rundunar hadin guiwar sojojin tarayyar Habasha da kawayenta na Eritrea.
KARANTA WANNAN LABARIN: Daliban Iran Sun Yi Arangama Da ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma A Tehran
Sai dai har yanzu gwamnatin Habasha ba ta ce uffan ba kan wannan batu.
Duk da kiraye-kirayen da ake yi na a dakatar da rikicin, Amma rahotanni na nuna cewa, ana ci gaba da gwabza fada tsakannin mangarorin biyu.
A WANI LABARIN KUMA: FG: Ba Mu Fitar Da Jerin Sunayen Wadanda Za A Karrama Na Kasa Ba
Jerin sunayen mutanen da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo da ake yadawa don karramawa ta kasa, karya ne, a cewar gwamnatin tarayya.
Marigayi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, da wasu sunayen mutane 436 sun shiga jerin a yanar gizo a karshen mako