By Ishaq Dabai
Mutane biyar sun mutu sakamakon tashin gobarar tanka a garin Mubi dake arewacin jihar Adamawa.
Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta fara ne a gidan mai da sanyin safiyar ranar Laraba lokacin da ake jigilar man fetur daga tankar man fetur kai tsaye zuwa daruruwan jarkoki a Kasuwan Gyela.
Mazauna garin sun shaida wa wakilinmu cewa akalla mutane biyar sun kone kurmus sakamakon gobarar, yayin da da dama suka samu raunuka.
Wani ma’aikacin agaji, Adamu Madobi, yace ‘yan uwa uku sun mutu a cikin lamarin.Madobi ya kara da cewa, “Fiye da babura uku da aka ajiye a kusa da gidan man sun lalace a gobarar.”
Babban Sakataren Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa, Dakta Muhammad Sulaiman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace mutum uku sun mutu yayin da wasu biyu ke karbar magani a asibiti.