Kamar yadda za a ga a manyan ma’aikatu na gwamnati da kuma kamfanonuwa wajen biyan albashi mataki mataki ne Inda za a ga wani yafi wani ɗaukan albashi haka kuma wasu ma’aikatun sunfi biyan albashi da tsoka.
To haka ma tana faruwa a duniyar ƙwallon ƙafa dama duniyar sauran wasanni da ake dasu daban-daban a faɗin duniya, haka a duniyar
ƙwallon ƙafa akwai jerin ‘yan wasan da suka fi ɗaukan albashi a sassa daban-daban na duniya wanda sun ninka wani ɗan wasan gida ashirin wajen ɗaukan albashi.
Ga jerin sunayen ‘yan wasa guda 10 da suka fi kowa ɗaukan albashi a shekarar da ake ciki ta 2020 a duniyar ƙwallon ƙafa:
1. Leonel Messi na Barcelona ana biyansa $126 miliyan.
2. Christiano Ronaldo na Juventus ana biyansa $117 miliyan.
3. Neymar na Paris Saint Germain ana biyansa $96 militant.
4. Mbappé na Paris Saint Germain ana biyansa $42 miliyan.
5 Mohammed Salah na Liverpool ana biyansa $37 miliyan.
6. Poul Pogba na Manchester United ana biyansa $34 moliyan.
7. Antoine Griezmann na Barcelona ana biyansa $33 miliyan.
8. Gareth Bale na Rrak Madrid ana biyansa $29 miliyan.
9. Robert Lewandowski na Bayern Munich ana biyansa $28 miliyan.
10. David De Gea mai tsaron gidan Manchester United ana biyansa $27 miliyan.