Gasar zakarun nahiyar turai gasa ce da aka fara ta tun a shekarar 1956, kuma gasa ce wadda sai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta sami wani mataki na cancantar buga gasar tun daga gasar rukuni-rukuni ta ƙasar ta da take bugawa wato idan tazamo matsayi na 1 ko na 2 kokuma matsayi na 3 sannan zata sami tikitin buga gasar ta zakarun turai, sai dai wannan gasa ba kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce take samun damar samun tikitin bugawa ba duba da cewar wata ƙungiyar ƙwallon ƙafan ko a jerin matsayi na ‘yan goman farko bazaka ganta ba.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona dake ƙasar Andalus ƙungiya ce data saba buga gasar zakarun ta turai kuma ta lashe kofin da dama, sannan tayi jerin ‘yan wasan da suka fafatamata wannin gasar ta zakarun turai inda wasu sun bayar da gudun mawa wajen jefa ƙwallaye sosai a raga a tarihin ƙungiyar tun daga fara zuwanta zuwa gasar zakarun nahiyar ta turai.
Ita dai Barcelona ta kwashe shekaru 30 tana fafata gasar zakarun nahiyar turai inda a iya tsawon shekarunnan ta buga wasanni 319 inda ta lashe wasanni 188, sannan tayi rashin nasara a wasanni 58 ta kuma buga kunnen doki a wasanni 73.
Sannan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta buga wasan ƙarshe sau 8 inda ta lashe kofin sau biyar a shekarun 1992 da 2006 da 2009 da 2011 da kuma 2015. Sannan a shekarun datayi rashin nasara awasan ƙarshen akwai 1961 da 1984 da kuma 1994.
Sannan itadai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona tazo wasan kusa dana ƙarshe wato semi final har sau 17 tunda ta fara fafata gasar ta zakarun nahiyar turai.
Ga jerin ‘yan wasan da sukafi jefa ƙwallo a matsayinsu na ‘yan wasan Barcelona a gasar zakarun nahiyar turai:
1. Leonel Messi ya jefa ƙwallaye 115.
2. Luis Suárez ya jefa ƙwallaye 25.
3. Rivaldo ya jefa ƙwallaye 22.
4. Neymar ya jefa ƙwallaye 21.
5. Patrick Kluivert ya jefa ƙwallaye 20.
6. Luis Enrique ya jefa ƙwallaye 19.
7. Samuel Eto’o ya jefa ƙwallaye 16.
8. Pedro ya jefa ƙwallaye 15.
9. Ronaldinho ya jefa ƙwallaye 14.
Daga cikin jerin ‘yan wasan da aka lissafa dukkaninsu basa tare da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona sai dai Leonel Messi kawai, inda ya zuwa yanzu ya bugawa Barcelona wasanni 143 a gasar zakarun nahiyar turai tun daga shekarar 2005 daya fara bugamusu wasa.