A yayin bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci jama’a da ‘yan siyasa su zama wakilan zaman lafiya.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Gwamnan ya yi wannan kiran ne a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, a yayin wani fareti na murnar samun ‘yancin kan Najeriya.
“Wannan bikin na musamman da kasarmu ta cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, shi ne na karshe a wannan gwamnatin. A shekara mai zuwa za a samu gwamnati ta daban, don haka ina so in yi amfani da wannan dama domin in gode muku dukkan mutanen Kano nagari.
“Ina kira ga ‘yan siyasa da su yi taka-tsan-tsan da munanan kalamai da kuma wasu munanan dabi’u da za su dagula zaman lafiyar al’umma a lokacin yakin neman zabe. Bari in yi amfani da wannan damar in yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da juna. Najeriya kasa ce da ke da kabilu daban-daban, addini da al’adun gargajiya.
KARANTA KUMA: Bazan Bari A Yi Amfani Da Kabilanci Wajen Tarwatsa Zaman Lafiyar Kano ba
“Duk da wannan, Allah da ya halicce mu ya kawo mu mu rayu da fahimtar juna. Ci gaban da muke samu a kasar, mu yi godiya yayin da inda muka samu kuskure, ya kamata mu yi tunanin mafita.”
A nasa bangaren, Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, wanda ya shirya taron addu’o’i na musamman ga kasa a fadarsa, ya dora wa matasa aiki da su zama jakadun samar da zaman lafiya da kuma kaurace wa duk wata daba ta siyasa da sauran miyagun ayyuka da ba a so.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ya kuma yi kira ga jama’a da su rika lura da kalaman nuna kiyayya saboda zaben 2023 na gabatowa.
A wani labarin kuma: Gwamnatina Ba Za Ta Lamunci Siyasar ‘Yan Daba Ba – Gwamna Sule
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya gargadi dukkanin jam’iyyun siyasar jihar da su yi siyasa ta hanyar da za ta kara wa masu zabe kima, yana mai shan alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da siyasar ‘yan daba da adawa da rarrabuwar kawuna a fadin jihar ba.
Sule ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da su bi ka’idojin dimokuradiyya da bin doka da oda da kuma bin dokar zabe.