Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar NNPP, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya wato yankin Igbo, zai yi asara a siyasance in dai bai haɗa gwiwa da NNPP ba.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Asabar a jihar Gombe a yayin ƙaddamar da sakatariyar NNPP a jihar.
Ya yi nuni da ƙalubalen siyasa da yake fuskantar yankin Kudu Maso Gabashin Najeriyar, yana mai ƙarawa da cewa ya kamata yankin ya fuskanci ƙalubalen a siyasance.
Kwankwaso ya ce yankin bai yi dabara ba a siyasance, kuma zai iya tafka asara.
Ya ce: “Ina son mutanen Kudu Maso Gabas saboda Ƙwankwasiyyar da kuke ji, da yawansu suna tunanin ta Okonkwo ce da ‘ya’yansa. Suna cewa saboda Bahaushe ba zai iya cewa ‘Okonkwo and sons’ ba, shi yasa yake cewa Kwankwaso.
“Kudu Maso Gabas yana da kyau ta ɓangaren kasuwanci, suna da ƙoƙari matuƙa, amma fannin da ya kamata su koya shi ne siyasa. Suna ƙasa sosai a wannan ɓangare.
“Idan ka kalli yanayin, sun rasa APC da PDP; ba su da Shugaban Ƙasa, ba su da Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Damar da suke da ita kaɗai ta iya zama Shugaban Ƙasa ko Mataimakin Shugaban Ƙasa shi ne su shiga NNPP. Arashi kuma, Igbo ne daga Anambra ya yi wa jam’iyyar rijista”, in ji Kwankwaso.