Rundunar Yansandan Jahar Nasarawa tace ta kama wani Mai suna Timothy Emmanuel, Sojan gona dake addabar mazauna Kananan Hukumomin Karu da Lafia na Jahar Nasarawa.
Kwamishinan Yansandan Jahar CP Adesina Soyemi, ya bayyana haka a ranar Juma’a a Lafia, a lokacin da yake gabatar da mai laifin da wasu guda 60 da suka aikata laifuka daban-daban.
Ya bayyana cewa, Mai laifin, wanda ya kasance Dan Asalin Jahar Filato, Yana cikin jerin wanda Rundunar Yansanda ke nema ruwa jallo, an kamashi ne akan hanyar B.A.D a Lafia a lokacin da yake kokarin tserewa a cikin wata mota kirar Corolla da Lambar Abuja BWA 973 CD, inda ake zargin shi da satar ita kanta motar, kamar yadda Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita
KARANTA WANNAN LABARIN: ManjoDatong Da Akayi Garkuwa Dashi A NDA Ya Shaki Iskar ‘Yanci
“Wani Timothy Emmanuel Dan kauyen Chiyawa a Karamar Hukumar Quanpan, wanda ya kasance a cikin jerin wanda Rundunar ke nema ruwa jallo ta samu nasarar kama shi.
“Dan shekaru 28 ya kasance yana Sanye da kakin soji gami da bindiga kirar AK-47 da kwafsar harsashi guda biyu.
“Wanda ake zargin bai taba kasancewa Soj, amma ya samo kakin Sojan ga kawunsa, wanda ya kasance shima Soja ne dayake aiki a Jahar Borno.
“An umarce ni cewa, sashen kula da masu aikata manyan laifuka zai cigaba da gudanar da bincike,” inji CP Soyemi.
Kwamishinan Yansandan ya kuma gabatar da wasu wadanda ake zargi da lalata hanyar jirgin kasa daga Jenkwe ta Karamar Hukumar Obi, tare da wasu kayayyaki dauke zuwa wani wuri da ba’a San ko Ina zasu je ba a cikin Jahar.
“Dukkanin wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata laifin, Kuma za’a cigaba da gudanar da bincike akan lamarin.
CP Soyemi ya bayyana cewa, ababen hawa guda 4 da muggan makamai guda 5, da wayoyin hannu guda 5 gami da harsashi guda 4 da Na’ura Mai kwakwalwa guda 1, na daya cikin abubuwan da aka samu daga gare su.