Yanzu an wuce Zamanin magudin zabe – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi alkawarin tabbatar da kare kuri’un da ƴan Najeriya suka kaɗa a zaɓukan da ke tafe, inda ta ce zamanin magudin zaɓe ya wuce.
Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wannan alkawarin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kaddamar da rahoton Yiaga Africa Election Analysis Dashboard, ERAD akan tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo, a zaben Ekiti da Osun na 2022 a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Wani Tsohon Dan Majalissar Wakilai Ya Rasu
Mahmood ya ce INEC ta yi aiki tukuru don inganta gaskiya da kuma kara kwarin gwiwar ‘yan Najeriya kan yadda ake gudanar da sakamakon zaben.
“Zan iya da karfin gwiwa cewa kwanakin magudin zabe ba bisa ka’ida ba sun kare a fili.
“Duk da haka, ba mu tsaya kan bakanmu ba, sanin cewa dole ne mu ci gaba da yin matakai da dama a gaban masu neman kawo cikas ga tsarin kuma akwai miyagu da dama a fagen kokarin kawo cikas ga tsarin, amma mun tsaya ne da adalci a zabe.
“Za mu tabbatar da cewa an kare kuri’un da ‘yan Najeriya suka kada kuma shi ne kadai wanda zai tabbatar da wanda zai zama me a dimokuradiyyarmu,” in ji shi.
Ya kara da cewa adadin ma’aikatan wucin gadi da hukumar za ta tura domin gudanar da zaben 2023 ya zarce yawan jami’an ‘yan sanda da na sojoji.
A wani labarin kuma: Yan bindiga Sun Hallaka Mutum Guda, Tare Da Jikkata Wasu A Kogi
Ana fargabar an kashe mutum daya, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ‘yan kasuwa a Ofeapo kan titin Idrisu-Bagana a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi.
Daily Trust ta ruwiato cewa, Wani ganau ya bayyana cewa an yi wa ‘yan kasuwar kwanton bauna ne a yayin da suke komawa gida daga Kasuwar Bagana da misalin karfe 8:30 na daren ranar Alhamis.