Wani mutum wanda ya yi sauye-sauye daban-daban a jikinsa don ya dena kama da mutane ya bayyana yadda yanzu haka ko gidan cin abinci ya je ba a siyar masa, Dailymail ta ruwaito.
KU KARANTA: Kotu ta umarci biyan diyyar N1.5m ga wata mata bayan an yi mata sharrin maita
Anthony Loffredo, mai shekaru 33 daga kasar Faransa yana da burin dena kama da mutane inda ya lallaba wurare daban-daban don ya sauya halittarsa.
Ya sa a cire masa kunnuwansa, hancinsa tare da datse yatsunsa musamman don ya yi kamannin da yake da burin yi.
Yayin hira da LadBible TV, mutumin ya bayyana yadda sauya halittarsa ta ke janyo masa caccaka ta ko ina inda hart gidajen abinci suka dena siyar masa.
Ya yi wadannan sauye-sauyen ne saboda yana jin tamkar an haife shi cikin wadanda bai dace da su ba.
Ya bayyana yadda sauya halittar tasa ta sa masa farinciki mara misaltuwa inda ya ce bai damu da maganganun mutane ba.
Anothony ya riga ya cike jikinsa da zane har da kwayar idonsa. Ya kuma bayyana yadda dakyar ya samu aikin yi da farko-farkon sauya halittar tashi.
Dole ciki ya sadudar da ke: Hotunan yadda halittar wata mata sauya bayan ta samu juna biyu
Wata mata ta wallafa bidiyonta kan yadda halittarta ta sauya gabadaya sakamakon yadda ta samu juna biyu, Legit.ng ta ruwaito.
Matar mai suna Haeyosato ta wallafa bidiyon ne a ranar Juma’a, 16 ga watan Disamba, inda nan da nan ta samu adadin kallo miliyan 7.5.
A bidiyon, Heyosato ta nuna yadda a baya take da kyau kafin ta samu ciki da kuma yadda ta koma bayan ta samu cikin.