Yanzu lokacin mai dawa kura aniyar ta ne, dole Buhari ya yi wa Tinubu kamfen – Onanuga
Saura mako guda da gudanar da zaben shugaban kasa, mai magana da yawun Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu, Shettima Bayo Onanuga, ya dage cewa shugaban nasa ya cancanci goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Bayanin hakan na kunshe ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC Ta Fara Siyar da Fom Din Tsayawa Takarar Gwamnan Bayelsa, Kogi, Da Imo
Onanuga ya yi nuni da cewa, Tinubu ya yi wa Buhari yakin neman zabe a 2015, inda ya kara da cewa shi (Buhari) ya kamata ya yi ma Tinubu a yanzu da ya ke takarar shugaban kasa.
Ya rubuta, “Tinubu sannan a shekarar 2014/2015 ya yi wa Muhammadu Buhari yakin neman zabe a Abeokuta. Ya kamata ya zama lokacin mai dawa kura aniyar ta ne.
A wani labarin kuma: Karancin Naira: Kai Jarumi ne na wannan lokacin – FFK ya yabawa El-Rufai kan caccakar Buhari
Jigo a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai kan matakin da ya dauka kan manufofin babban bankin Najeriya, wato Naira.
DAILY POST ta tuna cewa bayan sake fasalin takardar kudin Naira, babban bankin Najeriya, CBN ya sanya ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin wa’adin ci gaba da yaduwa.