Yanzu Lokacin Yarbawa ne su Mulki Najeriya — Inji Tinubu
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa kuma Jigon Jam’iyyar APC Bola Tinubu a ranar Alhamis yace yanzu lokaci ne da yarbawa zasu samar da Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.
Tinubu, ya bayyana haka a ɗakin taro na Shugaban Ƙasa dake Abeokuta, Jahar Ogun, a lokacin da yake jawabi ga Deliget na APC, gabanin Zaɓen Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Osinbajo na ganawa da Shugaban APC, da Gwamnoni 5
Tinubu, Wanda ya bayyana cewar yanzu lokacin Yarbawa ne, ya bayyana cewa lokacin shi ne ya zama Shugaban Ƙasa.
A jawabin shi, “wannan lokacin, lokacin yarbawa ne, kuma itace lokaci na.”
Jagoran Jam’iyyar ya samu rakiya zuwa Jahar Ogun Gwamnan Jahar Lagos Babajide Sanwa-Olu, da takwaran sa Umar Ganduje, da Tsohon Gwamnan Jahar Borno Kasim Shettima.
Yayi nuni dacewar shine ya sanya Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya dauki Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar sa.
Tinubu yace badan Allah dashi ba, Gwamnan Jahar Ogun Dapo Abiodun bazai zama Ɗan Takarar Gwamna kuma wanda ya samu nasara a Shekarar 2019 a Jahar .