Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi na Ƙasa Birgediya-Janar Buba Marwa mai ritaya, yace yanzu masu safarar ƙwayoyi sai sun tuntuɓi bokaye da ƴan tsubbu akan yadda zasu gudanar da aikin su.
Wanda a cewar sa, daga watan Disamba na Shekarar 2021, Hukumar zata ɗauki mummunan mataki ga shigowa da tabar wiwi a Nigeria.
Marwa ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin wani jawabi ga taron Manema Labaru, da Kwamitin Shugaban Ƙasa akan Sadarwa ya shirya a Villa, Abuja.
Shugaban Hukumar ya bayyana cewar, sai sun buƙaci an sanar dasu ranakun Sa’a da zasu wuce da ƙwayoyin su ba tare da an kama su ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nnamdi Kanu yace bashi da laifin komai, an ɗage shari’ar zuwa 10 ga watan Nuwamba
Yace ya sanya hannu da dama da ƙasashen waje akan yadda za’a magance shigowa da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
Comments 1