Yanzu Najeriya ce ƙasa ta biyu data fi kowace ƙasa fama da ta’addanci- Jihad Analytics
Kungiyar Binciken Ta’addanci ta Duniya, wato Jihad Analytics, ta ce Najeriya yanzu ita ce kasa ta biyu da kungiyar ta’addanci mai rajin Kafa ƙasar musulunci ke addaba a faɗin Duniya.
Ƙungiyar Bincike kan Jihadi ta ƙware wajen tattara bayanai kan ayyukan ta’addanci a Duniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya kara Kuɗin Tafiye-tafiye ga Ministoci, Manyan Sakatarori da sauran su
Alkalumman da kungiyar Jihad Analytics ta fitar sun nuna cewa, Iraki ce ta zo kan gaba, inda Najeriya da Syria suka zo na biyu da na uku.
Rahoton dai na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Najeriyar ke yawan ikirarin cewa an rage wa ƴan ta’adda ƙarfi akan ayyukan ta’addancin da suke yi.
Rahoton ya bayyana cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2022, kasar Iraki ta sami mafi yawan hare-haren ta’addanci a 337, yayin da Najeriya ta samu hare-hare 305 idan aka kwatanta da na Siriya 142.
Binciken da Jihad Analytics ta yi ya nuna cewa kungiyoyin ta’addanci na Boko Haram da ISWAP ne ke da alhakin kai hare-haren.
A wani labarin kuma: Yayin da Rikicin PDP ke ƙara ta’azzara, Wike, Ortom, Makinde sun sake ganawa a Landan
Yayin da rikicin jam’iyyar PDP ke kara taɓarɓarewa, Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, da takwarorinsa na jihar Benue da Oyo, Samuel Ortom da Seyi Makinde sun sake ganawa a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Duk da cewa ba a bayyana cikakken bayanin taron na ranar Juma’a ba, masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin yana da alaka da rikicin da ke cikin jam’iyyar PDP